Labarai

Ku taimaka ku tsamo mu daga mawuyacin halin da mu ke ciki, Ukraine ga Najeriya

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bukaci Najeriya, Kwaddibuwa da sauran kasashe na yankin Afirka su tallafawa kasarsa akan rikicin da ke aukuwa tsakaninta da Rasha wanda ya ki ci ya ki cinyewa, Aminiya ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana, sun dade da tattaunawa da shugabannin kasashen guda biyu da wasu na yankin Afirka don ganin sun gina alaka mai kyau ta tattalin arziki.

Yayin taron manema labarai wanda su ka yi ta yanar gizo ranar Alhamis, shugaban ya ce kudaden jarin da kasarsa ta zuba a kasashen yankin Afirka za su habbaka tattalin arzikinsu tare da samar da wadataccen abinci.

Ya ci gaba da cewa:

“Mun yi waya inda mu ka tattauna da shugabannin kasar Najeriya da kwaddibuwa da wasu kasashen daban-daban. Na yarda da cewa duk da yanayin yakin da muka tsinci kanmu, ya dace ace akwai alakar cinikayya mai kyau tsakaninmu.

“Abu ne mai matukar wahala a samu daga wurinmu amma zai yi dacewa ace kasashen Afirka sun hada kai don samar wa kawunansu mafita a bangaren wadatar abinci.

“A halin da muke ci, ba za mu iya shiga kasuwannin Afirka ba kasancewar Rasha ta toshe ko ina, amma duk da haka za mu iya ganin akwai hanyoyin cinikayya wadanda za mu iya yin amfani da su.”

Yayin da aka tambaye shi lokacin da yake hasashen yakin da ke tsakaninsu da Rasha zai zo karshe, cewa ya yi har sai lokacin da duniya ta tallafa musu.

A cewarsa:

“In har Putin ya ki mubaya’a, za a yi fama da karancin abinci. Hakan kuma zai shafi gaba daya duniya. Duk da cewa ba mu muka fara kai farmaki a yakin ba, amma za mu iya kawo karshensa.

“A matsayina na shugaban Ukraine, na nemi tattaunawa a lokuta daban-daban, amma duk da haka sun yanke shawarar halaka mu bayan mamaye mu. Bai dace hakan ya ci gaba da faruwa ba. Ya kamata kashen Afirka su hada kai wurin tallafawa Ukraine.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button