Labarai

Kotu ta yanke wa wani matashi daurin shekara 1 a gidan yari bisa laifin satar akuya

Advertisment

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Kano, a yau Litinin, ta yanke wa wani matashi dan shekara 23, Sadiq Miko, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar akuya, da kuɗin ta ya kai Naira 40,000. Daily Nigerian Hausa na wallafa a shafinsu

Miko, wanda ke zaune a Tudun Murtala Quarters Kano, an same shi da laifin sata.

Alkalin kotun, Zubairu Inuwa, ya baiwa wanda ake tuhuma zaɓin biyan tarar Naira 30,000 bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Inuwa ya kuma umarci mai laifin da ya biya wanda ya shigar da karan kudi naira 40,000 a matsayin diyya na akuyar ko kuma ya yi zaman gidan yari na watanni tara.

Advertisment

Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Ahmed Sarki, ya shaida wa kotun cewa wani Isah Bello na unguwar Ranji Kano ne ya kai karar a ofishin ‘yan sanda na Gwagwarwa Kano a ranar 10 ga watan Yuli.

Sarki ya ce a wannan ranar, da misalin karfe 10 na safe, wanda ake kara ya sace akuyar wanda ta kai Naira 40,000 a gidansa da ke Ranji Kano.

Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 287 na kundin laifuffuka.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button