Masha Allah ! Korafi Zuwa Ga Baba Buhari Mai Gaskiya – Datti Asaalafy
Ina yiwa Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya fatan alheri
Bayan haka Maigirma shugaban Kasa talakawanka suna korafi cewa tallafin da gwamnatin Nigeria take rabawa domin a saukakawa al’ummah saboda halin kunci da ake ciki a dalilin Coronavirus tallafin bai isa zuwa garesu
Ko ni nan Datti Assalafiy a labarai da hotuna nake gani wakilanka suna raba tallafi, amma ban taba ganin tallafin da idona ba, kuma a gaskiya talakawa suna kuka sosai musamman a jihohin da aka haramta musu fita neman abincin da zasuci su rayu
Shugaba Buhari ya kamata ka saka ido sosai domin hakkin talakawan Nigeria ya isa garesu lungu da sako, a kuma cire ra’ayin banbancin jam’iyya na siyasa, sanin kanka ne cewa akwai mahinta kuma azzalumai maciya amana da suke maka zagon kasa
Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka bashi ikon aikata daidai Amin