Labarai

Mawaƙiya ta soki Buhari kan naɗa Ibrahim Gambari

Fitacciyar mawaƙiyar nan ta Najeriya Yemi Alade ta tsoma baki cikin harkokin siyasa inda ta soki Shugaba Muhammadu Buhari bisa nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

A ranar Laraba ne aka nada tsohon ma’aikacin difilomasiyyar wanda kuma ya taba zama ministan harkokin wajen Najeriya lokacin mulkin sojin Janar Buhari, a matsayin shugaban ma’aikatan fadar ta shugaban kasa.
Ya maye gurbin Malam Abba Kyari, wanda ya rasu a watan jiya sakamakon cutar korona.
Farfesa Gambari yana da shekara 75 a duniya kuma hakan ne ya sa mawakiyar take adawa da nadin nasa.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, Alade ta ce ” mai shekara 75 a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa? Allah Ya kare Najeriya.”
Da ma dai wasu masu lura da lamura na ganin ya kamata a bai wa matashi mai jini a jika wannan mukami musamman ganin yadda yake bukatar aiki ba dare ba rana.
Ko da yake masu sharhi na ganin Farfesa Gambari yana da dukkan kwarea da ake bukata wajen gudanar da aikin.
75 years old as chief of Staff. God save Nigeria.

— ?? #WOMANOFSTEEL ?? (@yemialadee) May 12, 2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button