AddiniLabarai

Ragon layya ya fi ragon rada wa jarirri suna falala a Musulunci – Sheikh Kabiru Haruna Gombe

Jaridar Dclhausa hausa ta tattauna da babban shehin malami ash sheikh kabiru haruna Gombe akan falalar layya inda yake fadin falalar ta musulunci.

Ash sheikh kabiru haruna Gombe yana mai cewa:

Layya sunnah mai karfi, manzon Allah s.a.w yayi layya har ma yayi a madadin al’ummar sa, yayi a madadin iyalansa , malamai sunce layya tafi ragon suna karfi .

Idan matarka ta haihu sai ga layya tazo kuma ragon ka guda daya, to a hakuri jaririn kar a yanka masa rago, ragon ayi layya da shi yafi lada yafi falala.

Zaka samu mutum ya haifi ‘ya’ya sunkai 9 ba wanda bai yankawa rago ba, amma yace bai taɓa layya ba, idan kayi magana sai yace bai samu dama ba, na’am sai an samu dama.”-inji Sheikh Kabiru Gombe.

Layya tana da lada da yawa duk wanda yayi layya yana da lada yawan adadin gashin ragon da ka yanka, jinin ragon kafin ya zuba a kasa sai ya zuba wuri na musamman da Allah zai karba.

Saurari sauran falalar layya da take a ciki a cikin wannan faifain bidiyo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button