Labarai

Ka fi su gaskiya dattijo, mutuwa ce kadai zata raba mu, Matashi ya jaddada kaunarsa ga Buhari

Advertisment

Wani ‘dan gani-kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mutuwa ce kadai za ta raba shi da shugaban kasan.

Idan za mu tuna, Sirajo Saidu Sokoto a shekaar da ta gabata ta yi bore tare da sanar da cewa baya tare da shugaban kasan bayan ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ‘yan uwansa maza har biyar a jihar Sokoto.

 

Saidu fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a kafara sada zumuntar zamani ta Facebook kuma an san ya kware wurin caccakar masu zukar shugaba Buhari da jam’iyyar APC.

A ranar Juma’a, 29 ga watan Yulin 2022, ya sake jaddada goyon bayansa da kauna ga shugaban kasan Muhammadu Buhari.

“Ka fi masu zaginka gaskiya dattijo. Mun yi alkawarin mutuwa ce kadai zata raba mu da Buhari,” ya rubuta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button