Labarai
Yanzu-Yanzu: Mutunen da ke kula da ƙabarin Manzon Allah ya rasu


Advertisment
Allah Ya yiwa mutumin da ke kula da ɗakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina, Sheikh Abdou Ali Idris rasuwa kamar yadda aminiya ta ruwaito.
Agha Abdou Ali Idris Sheikh, daya ne daga cikin mutanen da suka fi dadewa suna hidima a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina.


Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami ta sanar cewa, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar Litinin.
An gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Manzon Allah sannan aka kai shi makwancinsa na karshe.
Abdou Ali Idris Sheikh shi ne Agha na uku da ya rasu cikin shekaru 10 da suka wuce.
A baya yawan masu aikin Agha ya haura mutum dubu daya, amma a halin yanzu wadanda suka rage a raye ba su fi biyar.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




