Labarai

Kalli hotunan Auren dan Sarkin Zazzau da Yar sarkin Ningi da ake magana akai

Manuniya ta ruwaito A yayinda ake ta cece-kuce kan shigar da diyar sarki tayi a Kano wacce ke shirin aurar dan shugaban kasa Manuniya ta leka Kaduna inda shima dan Sarkin Zazzau Nuhu Bamalli ya angwance da diyar Sarkin Ningi a ranar Asabar da ta gabata 7 ga watan Augusta 2021.
Manuniya ta ruwaito iyalan Maimartaba Ahmed Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau da na mai martaba Sarkin Ningi Alhaji Dr. Yunusa Muhammad Danyaya sun hada ya’yansu Abdullahi Ahmed Nuhu Bamalli da Halima Shuaibu Ahmed Adamu aure wanda kuma tuni aka shafa fatiha.
An daura auren ne a fadar sarkin Ningi dake jihar Bauchi a ranar Asabar 7 ga watan Augusta 2021 da wajajen karfe 11 na rana.

Jama’a da dama sun yabawa yadda aka gudanar da wannan aure cikin mutunci da girmama addini da ala’ada duk da cewa Sarkin Zazzau shine mai sarauta ta daya a Kaduna.

Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamali Tare da Dansa Abdullahi Ahmed Nuhu Bamali

Kalli hotunan auren dan Sarkin Zazzau da diyar  sarki kenan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button