Kannywood

Alan waka ya fito Takarar Dan majalisar Jiha A karkashin Jam’iyyar A.D.P

A yau din nan ne majiyarmu ta samu wani labari wanda abun akwai ban mamaki duba da yadda fasta takarar shahararren mawakin nan Aminu Abubakar Ladan wanda anka fi sani da alan waka ya fito neman kujerar dan majalisar jiha a jihar kano a karkashin jam’iyyar ADP a mazabar Nasarawa  wadda Sha’aban sharada ya koma kuma yake neman takarar shugabancin kujerar Gwamnan kano.

Wanda tuni dai shima shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara shima ya koma jam’iyyar wanda mawakin ya nuna a shekarar 2023 wake da shinkafa zaiyi.

Majiyarmu ta samu wannan sahihin labarin daga abokan sana’arsa kuma sakatare na kungiyar 13×13 Abubakar Bashir Maishadda inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

@alan_waka
Kada ka yi taraddadi da abinda idonka ya nuna maka zahiri ne.

Lokaci na a cirata a fidda ɗan takara daga cikin mutane ya yi wakilci don Mutane.

Ka sa a ranka Mulki na Allah ne kuma yana baiwa wanda ya so.

Ka sami nutsuwa da karfin gwiwa akan Nassara ta jajirtattun bayi ce waɗanda suka kamaci kamata.

Muna neman goyon bayanku masoya, kamar yarda ɗimbin nasararo da suka faru suke kan faruwa da gudunmawarku da hannunku wannan karon ma muna neman goyon baya da Addu’a a duk inda kuka kasance.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button