Yadda aka yi bidiyon tsiraicina ya karade duniya – Safara’u
Matashiyar mawakiyar nan a arewacin Najeriya, Safeeya Yusuf, wadda aka fi sani da Safara’u, ta bayyana yadda wani bidiyon tsiraicinta ya karade duniya.
A watannin baya ne bidiyon tsiraicin Safara’u, mai fitowa a shirin Kwana Casa’in da Arewa24 ke shiryawa, ya fita duniya. Ga yadda hirar da Bbchausa na kasance
Bayan fitar bidiyon, masu shirya fim din sun dakatar da ita daga shirin lamarin da ya sa ta tsunduma cikin harkokin wakoki.
Sai dai wakokin nata suna tayar da kura inda ake ganin suna bata tarbiyya, ko da yake ta ce tana fadakar da jama’a ne.
A wata tattaunawa ta musamman da BBC Hausa, Safara’u ta bayyana yadda aka yi bidiyon ya fita a duniya da kuma wadanda take zargi da fitar da shi.
Matashiyar ta ce ta shiga mawuyacin hali bayan faruwar lamarin inda ta kai har wata uku ba ta fita ko waje ba, har ma ta kai ana jifan ta da duwatsu idan ta zo wucewa ta wani wuri.
Safara’u ta ce an haife ta ne a garin Kano, mahaifinta dan garin Yola, mahaifiyarta kuma ‘yar Jihar Borno inda ta ce zama ne ya kawo su Kano. Ta kuma yi karatu a garin Ibadan na Jihar Oyo, bayan sun dawo Kano kuma sai ta shiga makarantar sakandare.
Wasu sun ce madigo nake yi
Ta bayyana cewa mutane da yawa sun ce tayi abin ne domin tura wa wata kawarta da suke madigo tare inda wasu kuma ke cewa ta aika wa saurayinta bidiyon ne.
‘‘Na kan yi irin wannan bidiyo na ajiye a wayata saboda jin dadi ko na wani abu daban, kuma ni na sani kashi 70 cikin 100 na mata na irin wadannan bidiyo su ajiye a wayoyinsu”, in ji Safara’u.
Ta ce duk da cewa ba ta san wanda ya yada bidiyon ba, amma tana zargin wadanda take tare da su kamar kawayenta saboda tana yawan ba da wayarta ga mutane domin yin kira.
Ta ce dukkan ‘yan uwanta sun ce mata wannan kaddara ne na rayuwa kuma ta dau dangana, amma mutanen gari ke tsinuwa suka yi ta mata da kuma kiranta da sunan karuwa wanda har ta kai ga ta kusan toshe dukkan shafukanta na sada zumunta.
Yadda aka yi na shiga harkar waka
Safeeya Yusuf da aka fi sani a yanzu da Safa, ta ce tun tana karama tana da sha’awar yin waka wanda hakan ne ya sa a yanzu ta koma bangaren.
Ta kara da cewa ita da kanta take rubuta wakokinta, sai dai kawai idan ta rubuta wani baiti ba daidai ba sai wanda suke aiki tare wato Mr 442 ya gyara mata.
A kan abin da ya sa take yin waka da maza kuwa, mawakiyar ta ce har yanzu ba ta samu wata mace da za su yi waka tare ba kuma tana waka da Mr 442 ne saboda tun shekara uku da suka gabata ta san shi saboda kyakkyawar alaka da suke da shi.
Safeeya ta ce tana sanya kananan kaya ne saboda ta fi sakewa idan ta saka su sabanin atamfa wadda take dame jikin mutum sannan ta kuma taso ne a barikin sojoji saboda mahaifinta soja ne.
Ga bidiyon nan.
Ba na fuskantar kalubale wajen iyayena
Safara’u ta ce ba ta fuskantar wani kalubale daga wajen iyayenta saboda waka da ta fara a yanzu da kuma fim da take yi a baya dukkansu sai da ta nemi yardarsu kafin ta fara, inda kuma ‘suka ce na je nayi tun da sana’a ce kuma na kiyaye a kan duk abin da nake yi,’’. Ta ce tafi son wakar ‘Inda ass’ a cikin wakokinta.
Ta kuma kara da cewa maganar da ake yi cewa hukumar Hisbah ta gayyaceta ita dai bata san da wannan zance ba saboda kafofin sada zumunta ne kawai suka yi ta yayata batun.
Ina so na zama kamar Davido
Jaruma ta ce ita dama ba barin harkar fim ta yi ba illa kawai hutu da ta dauka domin mayar da hankali kan waka.
Ta ce a yanzu haka ma suna shirin fara wani fim mai dogon zango ita da abokin wakarta Mr 442, kuma su za su shirya fim din da kansu.
Safara’u ta ce babban burinta a rayuwa shi ne ta ga ta zama kamar shahararrun mawakan kudancin Najeriya kamar Davido da Burna Boy da kuma ganin ta sami kyautar mawaka ta duniya Grammy saboda ‘‘Mu nan arewa ban taba ganin wanda Kudu suka kira shi yaje yayi wasa, amma za ka ga an kira su Tiwa Savage da P-square da Rikado da sauransu’’.
Jarumar ta kuma ce tana da niyyar yin aure amma kawai ba ta yarda da maza saboda tsoron da suke ba ta.
Ta ce idan lokacin ya yi za ta yi aure.