Kannywood

Jarumi Ali Nuhu Ya Samu Lambar Yabon Gwarzon Diraktan shekara

Advertisment

Shahrarren jarumin fina-finan Kannywood da Nollywood, Ali Muhammad Nuhu, ya yanki tutar gwarzon diraktan shekara a taron bada lambar yabon City People Entertainment Awards na wannan shekaran.

Taron lambar yabon na aukuwa ne a kowani shekarar karkashin jagorancin mujallar City People ga jaruman Najeriya da Ghana.

Ali Nuhu jarumi ne kuma dirakta ne a fina-finan Kannywood da Nollywood.

Sauran wadanda suka samu lambar sun hada da Hafsat Idris, wacce ta ci taurariyar shekara; sai Abubakar Maishadda wanda yaci frodusan shekara da fin din da ya hada ‘Hauwa Kulu’.

Sauran Misbahi Anfara da Hassana Muhammad.

An gudanar da taron ne ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2019 a jihar Legas.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button