Labarai

Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB

Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda ‘yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.

Kamar yadda Soltune yace, ‘yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan. Legit na ruwaito

Ya wallafa hotunan kanwar shi a lokacin da wasu suka kawo ta gida da kuma lokacin da ta warware kamar ba ita ba a ranar 27 ga watan Yulin 2022.Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB

A wannan shaidar, kai tsaye zan je kan maganar abinda zan tattauna a kai, babu dogon labari. Shekaru shida da suka wuce, ‘yar uwata ta tashi ta bar gida haka kawai. A cikin wadannan shekarun, na rasa mahaifina da ‘yar uwata, mahaifiyata da ‘yan uwana suna shan wahala amma mun cigaba da addu’a da yarda da Ubangiji,” yace.

“Ana nan tafe, bayan mako daya da aure na samu sakon ‘yar uwata cewa wasu sun zo har gida sun ajiye kanwata kamar yadda hoton farko ya nuna.
“Ban yi kuka ba saboda babu wani gurbin nuna ragwanci, na gane cewa ba zan bar wannan haka ba. Sai na tuna wata addu’a ta da nake yi cikin dare. Na cigaba da ihu ina cewa “shaidan, ba za ka samu wannan ba”.

“Na kira wasu daga cikin abokaina, na tura musu hoto kuma nace su yi min addu’a. Na tura wa ‘yar uwata kuma nace ta dinga mata addu’ar kowacce safiya.

“Bayan wasu makonni, ta fara tafiya da magana, yayata ta kira ni a wata safiya ta ce ” mun je asibiti bayan an duba ta, likita yace TB ya tafi hakazalika Kanjamau din”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button