Labarai

YANZU-YANZU: Gwamnatin Nijeriya ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin Boko Haram da ISWAP

YANZU-YANZU: Gwamnatin Nijeriya ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin Boko Haram da ISWAPGwamnatin Nijeriya ta ce ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar har guda 96, musamman ma waɗanda su ke goyon bayan Boko Haram da ISWAP.
Ministan Yaɗa Labarai na Ƙasa, Lai Mohammed ne ya baiyana hakan yayin ganawa da manema labarai a kan irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu na yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.
Ya ce “A nata ɓangaren, a nazarin da Hukumar Hada-hadar Kuɗi ta Sirri ta Ƙasa, NFIU, a 2020-2021, ta bankaɗo masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya, abokan harkar masu ɗaukar nauyin ta’addanci su 424, da sa hannun wajen kamfanunuwa 123 da kuma kamfanonin canjin kuɗi 33, gami da baiyana ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane 26 da kuma masu taimaka musu guda 7.
“Nazarin ya haifar da kama mutane 45 da kwanan nan za a yanke musu hukuncin a kotu da kuma kwace kadarorin su.
“game da ɗaukar nauyin ta’addanci, NFIU na musayar bayanan sirri da kasashe 19 a kan Boko Haram, ISWAP, fashin daji da garkuwa da mutane.
“Da ga lokacin 2020-2021 NFIU ta maida kuɗaɗen damfara da su ka kai dala 103,722,102.83, 3,000, fam 7,695 da kuma dalar singapore 1,091 ga ƙasashe 11,”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button