Yanzu-yanzu: Hukumar PPPRA ta goge sanarwar da tayi na karin farashin mai
Hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan arzikin mai a Najeriya ta goge sanarwar da tayi a shafinta na yanar gizo na karin farashin litan man fetur a Najeriya.
Hukuma ta sanar da kara farashin a shafinta a daren Alhamis, amma ta goge da safiyar Juma’a sakamakon kalaman jama’a.
Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya sake jaddada cewa ba za a kara farashin litan man fetur a watan Maris ba duk da tashin da farashin danyen man yayi a kasuwar duniya.
Wannan ya biyo bayan rahoton hukumar sanya farashi da kasuwancin mai a Najeriya PPPRA wanda yayi hasashen cewa farashin mai a yanzu na iya tashin N212 ga lita.
A sakon kar ta kwana da NNPC ya aike, yace:
“NNPC na jaddada cewa babu kari a farashin man fetur na Ex-Depot a watan Maris.”
Source: legit