Labarai

Ka bar batun kamfen, fara kulawa da lafiyarka, Kwankwaso ga Tinubu

Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar NNPP ya shawarci dan takarar APC, Bola Tinubu akan ya mayar da hankalinsa kan lafiyarsa, Legit.ng ta ruwaito.

Ya yi wannan maganar ne yayin tattaunawa da Reuben Abati na Arise TV a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin, inda shugaban NNPP din ya ce ya kamata Tinubu ya duba lafiyarsa.

Kamar yadda yace:

“Idan kun ga abokina, Bola, kuce masa yabi a hankali ya kula da lafiyarsa ya kuma tabbatar ya….. saboda ina sonsa sosai, abokina ne,” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa:

“Kamfen na da wahala kuma akwai bukatar mutum ya dage kwarai. Ina fatan zai bi a hankali don a asamu a gina kasar nan dakyau ta samu ci gaba.”

Akwai mutanen da su ka dinga maganganu dangane da lafiyar Tinubu tun bayan ya bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa.

LH ta kara da cewa A watan Augustan 2021, an samu maganganu akan matsanincin yanayin da yake ciki. Daga bisani kuma gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya musanta batun ciwon yace lafiyar Tinubu kalau.

Duk da maganganun amma hakan bai sa dan takarar ya sare ba daga kudirinsa na son shugabancin ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button