Labarai
Soyayya ruwan zuma: Bidiyon saurayi da budurwar da su ka yi musayar takalma
Wani guntun bidiyo ya dinga yawo a kafafen sada zumunta wanda aka ga wani namiji sanye da takalmin mata yayin da macen ke sanye da takalmin maza, Legit.ng ta ruwaito.
Ana zargin macen ta gaji da yawo da dogon takalmi ne namijin ya taimaka mata ta hanyar amsar takalmin kafarta ya sanya don su yi musaya. LH na wallafa
Wannan bidiyon ya dauki hankula wanda mutane da dama su ka dinga mamakin irin wannan soyayyar.
Yayin da wasu su ke ganin abinda yayi daidai ne, kuma soyayya ce ta janyo har ya fara tunanin taimaka wa macen daga wahalar dogon takalmin.
Bidiyon sakan 4 ne kacal wanda shafin mufasatundeednut ta wallafa. Ga bidiyon:
View this post on Instagram