Labarai

Rundunar yan sandan Kano ta kama wani Dan sandan bogi tare da kakin yan sanda (bidiyo da hotuna)



A Yau ta ruwaito rundunar ta samu koke kan yadda wasu ke yin sojan gona da sunan su yan sanda ne suna musgunawa al’umma da masu ababen hawa suna karbar kudade a hannunsu musamman a yankunan Sabon Gari, da Fagge, da Koki Quarters dake birnin Kano

Kakakin yan sandan Kano Kiyawa ya ce jami’ansu sun samu nasarar cafke wani Salisu Bala, dan shekara 31 a yankin Kurna Quarters sanye da kakin yan sanda kuma bayan anyi bincike aka gano ba jami’i bane sannan ko da aka zurfafa bincike sai aka gano ashe har dillancin ƙwayoyi yana yi sannan kuma aka samu kayan yan sanda kala huɗu a gidansa.

Ga hotunan.

Rundunar yan sandan Kano ta kama wani Dan sandan bogi tare da kakin yan sanda (bidiyo da hotuna) Rundunar yan sandan Kano ta kama wani Dan sandan bogi tare da kakin yan sanda (bidiyo da hotuna) Rundunar yan sandan Kano ta kama wani Dan sandan bogi tare da kakin yan sanda (bidiyo da hotuna)

Ga bidiyo.









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button