Labarai

Ban damu ba don yarana sun girma sun ga hotunan tsiraicina su na yawo a soshiyal midiya, Shugatiti

Shugatiti, jarumar kasar Ghana kuma ma’abociya bayyana tsiraici ta ce bata damu ba don a biyata kudi ta yi fim tsirara, DklassGh.com  LH sun  ruwaito.

A wata tattaunawa da aka yi da ita a Asempa FM, ta ce bata damu da caccakar mutane ba a kafafen sada zumunta saboda yanayin ayyukanta.

Ta bayyana cewa tana jindadi idan taga masoyanta su na yabawa da bidiyoyi ko hotunanta.Ban damu ba don yarana sun girma sun ga hotunan tsiraicina su na yawo a soshiyal midiya, Shugatiti

Shugatiti ta kara da cewa za ta iya yin tsirara akan kudi don tana ta samun makudan kudade ta kafafen sada zumunta.

Daga baya ta kalubalanci wani ya gwada bata $30,000 ya gani idan bata yi tsirara a tattaunar kai tsaye da take yi a kafar sada zumuntar Facebook ba.

Ta kara da cewa ko nadama ba za ta yi ba don yaranta sun girma sun ga hotunan tsiraicinta su na yawo a yanar gizo.

Kamar yadda tace:

“Zan iya fim tsirara idan aka biyani $30,000 kuma ba zan yi nadama ba don yarana sun girma sun ga hotunan tsiraicina suna yawo a yanar gizo ba.”

Har ila yau ta bayyana cewa tana soyayya da wanda ‘yan uwansa su ka san aikinta. Ta kara da cewa:

“Nan gaba zan yi aure. Ina soyayya da wani wanda ‘yan uwansa sun san tarayyarmu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button