Labarai

Ko Kun San Me Shugaba Buhari Ke Nufi Da Cewa Gwamnatinsa Za Ta Yi Tsauri A Wannan Karo?

Mai taimakawa shugaban Nijeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya yi wa BBC karin haske dangane da kalaman da shugaban Najeriyar ya yi a kan cewa wa’adin mulkinsa na biyu zai kasance mai tsauri.

Malam Garba ya ce shugaban yana nufin shekaru hudu masu zuwa ga shugaban ba masu sauki bane saboda daga wadannan shekarun babu saura.

Ya ce a fahimtarsa shugaban na nufin zai yi gwaninta ne wajen cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya.

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da ministocinsa a lokacin da suka kawo masa ziyara a fadar shugaban kasar domin taya shi murnar lashe zaben kasar.

Wa’adin mulkina na biyu zai kasance mai tsauri – BuhariAn kashe mutane da dama a ZamfaraAmurka ta taya Buhari murnar lashe zaben 2019

Wadannan kalamai na shugaban sun kasance kalamai masu harshen damo ga ‘yan Najeriya domin kuwa tuni jama’ar kasar da dama suka fara bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta dangane da fahimtar su a kan kalaman.

Ko da aka tambayi Malam Garba Shehu ko kalaman na shugaban na nufin cewa mutane za su ci kwakwa? Sai ya ce” ba haka bane, domin shi shugaba ba za a zabe shi ba don ya gallazawa al’ummar kasarsa ba, sai dai ya kyautata masu ya kyautata rayuwarsu.

ROHOTON BBC

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button