Rikicin Sojoji da matasa a unguwar Chake, ya yi sanadiyar rasa ran yaro 1 da raunata matasa 2 da sojojin suka harba a jihar Katsina


Kamar yadda bincike ya tabbatar ta bakin wasu mutane shaidun gani da ido waɗanda suka buƙaci a sakaya sunansu, sun bayyana cewa a wani ɓangare na unguwar chake, wasu fusatattun matasa suna sana’ar sayar da kwayoyi da kayan maye, to cikin waɗanda ke zuwa saye har da sojoji.
Aka yi rashin sa’a, a ranar asabar 23, ga watan Maris 2024. wasu sojoji sun tsaya saye kamar yanda suka saba, sai kawai aka ji rikici ya ɓarke tsakaninsu, su masu sayar da wannan kayan maye suka fiddo makamansu irinsu adda wuka da sauransu.
Kafin ka ce kwabo su kuma sojoji suka fara da harbe harbe daga bisani ana haka sojojin nan suka harɓi mutum ukku yaro 1 daga cikinsu ya mutu wanda ɗa ne ga Malam Umaru kucugu, da ke Unguwar Chake, a jihar Katsina, majiyarmu ta samu ta katsina Reporters sunka wallafa a shafinsu.
Ana cikin haka ne shi kuma wani soja ya taka sawun ɓarawo, bayan waɗancan sojojin sun tafiyar su, shi kuma ya taho saman mashin din sa, su kuma fusatattaun matasan suka bige shi suka kwace mashin ɗin sa suka kunna masa wuta wanda hakan yasa ya tsere domin ya tsira da rayuwarsa.
Bayan faruwar haka, sai wasu sojoji suka dawo aka cigaba da bata kashi tsakaninsu da matasan sai dai jami’an tsaron ‘yan sanda sun tarwatsa matasan ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa.
Wani ɗan kasuwa ya shaida cewa misalin karfe 8:00pm ya biyo titin Chake zuwa Kofar Guga ya hango wuta naci ya sha da ƙyar, inda matasan suka rufe hanyar har tsawon kusan awa guda ta hanyar kunna wa tayoyi wuta tare da baiwa masu ababen hawa umurnin ƙauracewa hanyar.
Haka kuma misalin karfe 8:40pm wani mazaunin unguwar chake ya bayyana cewa halin da ake ciki sun kasance cikin halin tagayyara ta inda tsoffi da Yara na sahun gaba wajen Fama da matsalar ɗaukewar nunfashin sakamakon, barkonon tsohuwa da aka harba acikin unguwarmu.
A cewar sa, hakan ya tilastawa wasu barin unguwar ‘yan kasuwa da yawa sun rufe shagunansu saboda tsoron abinda ka Iya faruwa na asarori.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





