Kannywood

Garabasa : Ku hanzarta wannan gagarumar damar ka ci gasar miliyan Daya

Call For Application.! Call For Application.!! Call For Application.!!!

Digital filmmaking workshop and contest, workshop ne da aka shirya wanda zai gudana cikin garin kano, na tsawon kwana hudu karkashin kamfanin Hanas International Films, wanda gidauniyar matasan Muhammad Abacha Awareness Network (MAAN) ta dauki nauyi.

Shirin zai bada damar horas da matasa kimanin dari biyu (200) sana’o’i daban-daban dake cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa, tare da kwararru a kowannne fanni.

Abubuwan da za a koyar sune :

a) Rubutun fim
b) Bada umarni
c) Tace hoto
d) dabarun rubutu da rera waka
e) shirya fina finai
f) Sarrafa camera, haske da murya
h) Dabarun acting (kwaikwaya)

A karkashin shirin, har ila yau, za’a gudanar da gasa a kowanne rukuni a matakin karshe, ta tsabar kudi naira Milyan daya (one million naira), ga wadanda suka yi nasara.

Damarmakin da wanda ya samu shiga tsarin zai samu :

1) Koyon sana’a don dogaro da kai
2) ilimin sanin menene film da kuma muhimmancin sa a duniyar mu ta yau.
3) Damar zamowa cikin zakarun da zasu samu kyautar Naira Milyan daya
4) Tarayya da manyan masana fina-finai.
5) Shaidar certificate na kammala workshop

Abubuwan da ya kamata kafin ka shiga ka sani :

1) Za a fara karbar application ranar ashirin ga watan biyar shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu 28/05/2022

2) Za a rufe karbar application ranar goma ga watan shida shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu 10/6/2022.

3) Za a kammala tare da tantancewa wadanda sukai nasarar shiga cikin tsarin zuwa ranar sha biyar ga watan shida ( 15/06/2022) sannan a sanar da kowa ta email dinsa ko ta number wayar da suka shigar.

4) Ga wadanda sukai nasarar shiga cikin tsarin zasu biya kudin register na naira dubu uku (3000).

5) Za a fara gudanar da karatun ranar ashirin ga watan shida (20/06/2022), zuwa ranar ashirin da uku ga watan shida (23/06/2022).

6) Ranar ashirin da hudu ga watan shida (24/06/2022) za a gudanar da gasa a tsakanin mambobin workshop din.

7) Taron zai gudana ne a cikin birnin kano.

8) Wurin taron da lokaci za a sanar da shine kai tsaye ga wanda suka samu nasarar shiga cikin tsarin ta hanyar email ko whatsapp ko sakon sms ta number da suka bayar a lokacin register.

Domin samun damar shiga cikin tsarin kai tsaye a cika form ta wannan link din dake kasa.

APPLY HERE

https://forms.gle/QJ8QAM2u4ACVxmjd8

Don karin bayani kai tsaye a tura sakon whatsapp ko sms ta wannan number
08122205091

Sadeeya Abdulqadir
Aliyu Muhammad Hanas
Hauwa’u Salisu
Real Nana Aisha
Rahma Sabo Usman

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button