Kannywood

Sarkin waka yayi martanin akan Masu zaginsa kan bidiyon wasa da daloli da yayansa

Biyo bayan wani bidiyo da fitaccen mawakin nan kuma jarumi a masana’antar shirye-shiryen fim ta Kannywood, wato Nazir M Ahmed, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya wallafa a shafin shi na Instagram yana nishadi da iyalin shi.
Bidiyon ya jawo kace-nace, sakamakon yadda aka nuno suna wasa da dala shi da matan shi da kuma ‘ya’yan shi.

Mutane sun yi caa akan Sarkin Waka

Al’umma sun yi caa akan wannan bidiyo a shafukan sada zumunta na yanar gizo, inda tilas ta sanya daga baya Mawakin ya goge bidiyon ya kuma mayer gurbin shi da wani rubutu.shafin labarunhausa ya tattara bayyanai.

Sarkin Waka
Nazir M Ahmed Sarkin Waka – Photo Source: @sarkin_wakar_san_kano
 

Rubutun da fitaccen Mawakin ya wallafa daga baya ya bayyana cewa:
“Ba a fariya da chicken change.”
Ma’ana a nan shine
 


 
Daga baya kuma jarumin ya sake shiga bangaren sharhi, inda ya sake wallafa wani rubutu a kasa ya ce:

“Kaidai Allah ya tsareka da wawa ya yankema hukunci!”

Ra’ayoyin mutane dangane da bidiyon

To sai dai kuma wannan bidiyo da ya dora tuni, tashar YouTube ta tsakar gida ta dauka ta wallafa a shafinta, inda mutane suka yi ta tofa albarkacin bakin su, ga kadan daga cikin abubuwan da mutane ke cewa:

“Sarki. A yadda muka sanka, da hankali, ilimi, da tunani be kamata kayi haka ba. Hakan dabi’an wasu yaran masu kudine marar tarbiyya wadanda basu san zapn kundinba. Kuma se gashi kana koyawa iyalenka. Hakika wasa da iyalii nada dadi, kyau da gwanin sha’awa, amma ba wasa da kudiba (Sarki). May it be first last and final. Fatan alkhairi ga wanan channel da al-umma baki daya. Ina mika ta’aziyana ga yan uwa Muslims in general, na rashi da mukayi na (MLM.DR. AHMAD BUK’ حدثنا’ Allah SWT ya gafarta masa ya masa rahma, ya sanya haske, ni’ima, da farinciki a ma kwancinsa da dukkan al-umman musulmae baki daya. وسلا م عليكم.
Naxeef YakSard

“Mashaa Allah, Sarkin Waka. Haka Ake so, a su a jika, a yi Wasa da dariya da su. Ko da duwatsu ma yiye dede wasan. They will grow with love and affection amongst themselves and they will love and remember you throughout their lives. Allah Ya Raya, Ya Dayyaba, Ya musu albarka. Duk da shauran Yaran Alumah Manzo (SAW).
Zainab Nuhu

“Allah ya bada lfy dan Allah yaya Umar a mika min sakon gaisuwa zuwa sarki dan abin ya birgani sosai wly naji daɗi har cikin raina,,❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️????????????
Abdul moumin maza baban halid

“Inason mutum mai wasa da iyalinsa, rana ta farko a duniyar nan danaji Sarkin waqa ya burgeni
Shamsuddeen Harun

“Aduka sadaka na kaiwa marayu ba adun ga nunawa adu niyba
Fathima Musa Abdullahi

“Wlh sai yanzu nasan baka da wayo wlh kuma baka aiki da hankalinki wlh
Meenat Abdul

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA