Kannywood

Matar Adam a Zango ta yiwa A.Zango Kalamai Wanda sunka Dauki Hankalin mutane

Jarumi Adam A. Zango da matarsa Safiya Chalawa sun cika shekaru uku da aure a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayun 2022 kamar yadda ta sanya a shafinta na Instagram.

Sun dinga yin wallafe-wallafe a shafukansu na sada zumunta su na nuna soyayya da matukar shaukin juna da su ke yi, wanda hakan ya dauki hankalin mutane da dama.

Sun dauki kyawawan hotuna sanye da kaya na gani da fadi tare da diyarsu, Diyana wanda hakan ya sa mutane su ka dinga yi musu sambarka.

LabarunHausa.com ta leka shafin matar Jarumin, Safiyya Chalawa na Instagram inda ta ga wani rubuto mai ratsa zuciya ta da yi wa mijinta akan kaunar da ta ke masa.

Ta fara da bayyana cewa mijin nata yana da abubuwa da dama da maza su ke nema amma sun rasa.

Ta ce tana matukar sonsa kuma da za ta iya rubuta littafi, za ta yi ne akan kyawawan halaye da fuskarka.

Kamar yadda ta wallafa:

“Hakika Allah ya wadata ka da abinda maza da yawa su ke nema sun rasa…

“Babu shakka maza irinka kadanne. Kai da ace na iya rubuta labari, da akan kyawun halinka da fuskarka zan rubuta labarin mai suna KYAUTA DAGA ALLAH.

“Kullum ina jaddada maka kalmar ina son ka domin wannan kalmar ita ce iyakar kurewar abinda bakina zai iya fadi akan soyayyarka.”

Ta ci gaba da fatan Ubangiji Allah ya bar su tare ya kuma tabbatar da soyayyarsu har abada.

Safeeyaa Chalawa ita ce matar jarumin ta biyar bayan rabuwar aurensa da Ameena Rani wato Maman Haidar, tsohuwar jarumar Kannywood, Maryam AB Yola da sauran matansa biyu.

Ya aure ta ne a shekarar 2019 kuma ita din ‘yar asalin Jihar Kebbi ce. Yanzu haka su na da diya daya tal.

Muna musu fatan alheri da kuma fatan auren nasu zai dore har sai mutuwa ta raba su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button