Zargin Lalata A Kanywood: Nafisa Abdullahi ta ƙalubalanci Naziru Sarkin Waƙa


Fitacciyar jarumar ta bayyana haka ne a yau Asabar a shafinta na Facebook. Kuma kalaman na ta suna zuwa ne a lokacin jarumai a masana’antar Kanywood ke zargin juna akan rashin adalci da kuma zalunci a tsakaninsu.
“A kowanne profession akwai matsaloli daban – daban da mutane ke fuskanta, akwai masu cuta, akwai kuma wanda ake cutarwa”
“Zantuttukan da Naziru Ahmad yayi babban zargi ne (Serious Allegations) ne da ba’a ɗaukan su da sanyi ko a ina ne, a ciki har da ‘Sexual Assault’ wanda shi ne dalilin da ya sa na saka kaina a cikin abinda bai shafe ni ba. Amma kuma idan aka yi la’akari da abinda ya faɗa, ya shafe ni tun da mace ce ni”.
“Idan abin da yake faɗa gaskiya ne kuma yana da hujjoji da kuma shaidu, ina cikin mutanen da su ke so su san su waye masu yin hakan”. In ji Nafisa Abdullahi
Haka kuma jarumar ta bayyana cewa a cikin dokokin Najeriya da ma waɗanda su ka kafa masana’antar Kanywood babu inda doka ta ce sai mutum ya yi lalata da mace dan zai sakata a cikin wasan kwaikwayo.
“Tun da ya faɗawa duniya cewa ga abin da ake yi, to ƙarshen adalci wa wanda aka zalunta shi ne mu san su waye? Kuma mu ɗauki mataki akan su, dan a cikin dokoki (Laws) din mu na ƙasar nan da kuma masana’antar Kanywood (Film Industry) ɗin babu inda aka ce sai mace ta kwanta da wani kafin a saka a fim (it’s acceptable to say a lady should sleep with you for films). Ta ce akwai tanadin hukunci mai tsanani ga wanda aka same shi da aikata haka. (There are consequences and the people who’re guilty should be seriously punished).”
Haka kuma jaruma Nafisa Abdullahi ta yi kira ga duk wata jaruma a masana’antar Kanywood da ta san haka ta faru a gareta da ta fito ta fadawa duniya domin ɗaukar matakin taƙaita cigaba da faruwar hakan.
“Daga ƙarshe kuma, duk macen da ta san an taɓa ce mata to give herself for films, fight for your rights and tell us su waye, because if you don’t speak up, ba za a taɓa samun gyara ba”.
A jiya ne dai Naziru Sarkin Waƙa ya yi zargin cewa ana zaluntar jarumai a masana’antar Kanywood inda ake biyansu Naira 2000 zuwa 4000 a wasu lokutan ma har sai ta kai ga jarumai mata sun bayar da kan su kafin a saka su a cikin shirin ɗin.





