Labarai

An kama tsohon shugaban hukumar yaki da cin-hanci ta Kano, Muhuyi Rimingado

Jami’an ‘yan sanda dauke da makamai sun cafke tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Rimingado.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa an kama Rimingado ne a masaukin Gwamnan Sokoto da ke Abuja, inda ya je a tantance shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP.

An jiyo cewa ƴan sandan sun tafi da Rimingado nan da nan bayan an tantance shi, inda su ka wuce da shi ofishin shelkwatar ƴan sanda ta Abuja.

Majiyoyi na tsaro sun ce za a wuce da shi Kano domin a gurfanar da shi a gaban kotu.

A ranar 28 ga watan Maris ne ƴan sanda su ka dira gidan Rimingado amma ba su samu nasarar kama shi ba.

A tuna cewa an dakatar da Rimingado ne a watan Yulin shekarar da ta gabata bayan buɗe bincike kan badaƙalar kuɗi da kuma aringizon kuɗaɗen kwangiloli da a ke zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da dangin gwamna.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button