Labarai

Bayan gwaji da tantancewa, fasto ya rabawa ‘yan matan cocinsa takardun shaidar budurci

Advertisment

Wata cocin Afirka ta kudu ta kaddamar da gwajin budurci ga ‘yan matan da basu yi aure ba yayin da ta bayar da takardar shaida ga wadanda su ka yi nasara, LIB ta ruwaito.

An shirya tantancewar ne don bayar da kwarin guiwa ga mata don su kasance masu kamun kai a cikin al’umma.

Cocin mai suna Nazareth Baptist tana Ebuhleni, yankin arewacin Durban a Afirka ta kudu.

An tattaro bayanai akan yadda cocin ta shiya tantancewa ‘yan matan da basu yi aure ba na cocin wadanda su ka kai shekaru 18 zuwa sama don gane budurcinsu.

Advertisment

A taron na ko wacce shekara wanda cocin ta shirya, da zarar an kammala tantancewa za a bayar da takardar shaidar budurcin ga duk wacce aka tabbatar da budurcinta.

Sannan akwai wani farin zane da ake yi wa ‘yan matan a goshi idan aka tabbatar da kamun kan su.

Ana yin gwajin ne a tsakiyar ko wacce shekara kuma da zarar lokacin ya zagayo na wata shekara, takardar ta baci, sai har an sake gwajin a cikin cocin.

A wannan makon ne aka gabatar da gwajin na shekarar 2022/2023 sannan aka bayar da takardar shaidar ga matan da suka wuce gwajin.

A jikin takardar akwai sa hannun shugaban cocin Nazareth Baptist wanda shi ne ke gabatar da gwajin.

Hotunan da su ka bazu a yanar gizo sun nuna yadda ‘yan matan da su ka wuce gwajin lafiya su ke ta murmushi yayin da su ke rike da takardar shaidar.

©Labarunhausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button