Labarai

Shin da gaske Limamin masallaci ya aje limanci saboda zai tsaya takara ?

Kamar yadda anka ta yayata wa a shafukan sada zumunta cewa wai wani limamin yace zai aje mukaminsa na limanci saboda takara kamar yadda ake yayatawa a shafukan sada zumunta.

Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA a Jihar Katsina ya ajiye muƙamin limancin sabo da zai tsaya takara.

A wasiƙar ajiye limancin da ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.

Shin da gaske Limamin masallaci ya aje limanci saboda zai tsaya takara ?
Takarda aje limanci

Wani ɓangare na wasiƙar, wacce Daily Nigerian Hausa ta gani ya ce, ” Ni Muhammad Hashim (Liman) na aje muƙami na na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA sabo da tsayawa takara da zan yi.

“Ina fatan Allah SWT Ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, Ya yafe mana kusa-kuren mu Amin.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ƴan kwamitin masallacin da ma al’umma baki ɗaya.”

To bayyan wannan alhamdulillahi limamin masallacin ya karya wannan maga ga abinda yake cewa.

Ina bisa abin hawa kafin na sauka naga kiraye kiraye sama da 20, kowa sai kira yake yaji ni liman Muhammad Hashim ake nufi na ajiye limanci? To A’a bani ba, asali ma ni ba limamin masallacin juma’a bane.

Yadda kuka tsinci takardar nan a social media nima haka na tsinceta har nayi posting, wasu dai ne kawai ke neman tada zaune tsaye. Saboda haka na barranta kaina da ita, bani da alaka ta kusa kota nesa da wannan batu.

Allah ya kara tsare mana mutuncin mu dana addinin mu Amin.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button