Labarai

Gaskiya ta bayyana: Ashe Abin Al’ajabi mutum ne ba aljani ba

A ko wacce shekara, hawan sallah na sarakunan gargajiya ya kan zo da abubuwa burgewa, nishadi da kuma kayatarwa.LH na ruwaito

Sai dai hawan sallar da ta gabata na Jihar Gombe ya zo da wani salo na daban wanda ya dauki hankalin mutane da kwarai.

A cikin tawagar Falakin Gombe an samu wani wanda shigarsa ta yi matukar bayar da nishadi kana ta tsoratar da wasu har ake zargin aljani ne.

Kamar yadda wadanda su ka je hawan su ka gani, ya je ne da wani salo irin na matsafa don hatta shigarsa ta yi matukar bambanta da ta saura sannan ya dinga sarrafa doki yadda ya ga dama.

Akwai lokacin da ya daura kada a kansa sannan ya sanya kaho kuma ya yi amfani da wasu abubuwa na daban har da fatun dabbobin da ba a sani ba.

Wannan lamari ya yi matukar daukar hankali har wa su suka nemi sanin ko shi wanene hakan ya sa LabarunHausa ta dinga bibiyarsa don gano gaskiya.

Gaskiya ta bayyana: Ashe Abin Al’ajabi mutum ne ba aljani ba
Gaskiya ta bayyana: Ashe Abin Al’ajabi mutum ne ba aljani ba

A watan da ya gabata Aminiya ta yi hira da shi inda ya ce daga wata duniyar ta daban ya ke kuma hatta kayan da ya yi amfani da su, ya samo su ne a waccan duniyar.

Sai dai kwatsam sai ga wani hotonsa ya bayyana, sanye da kayan makarantar boko kamar ko wanne dalibi inda aka ga ya dauki hoton tare da abokan karatunsa.

Duk wanda ya ga hoton zai gane cewa mutum ne shi kamar kowa kuma ya dauka ne a lokacin da ya ke makarantar sakandare kuma mun gano cewa sunansa Abdulrazak Abubakar.

Da alamu ‘wada’ ne kawai, kasancewar Ubangiji ya halicce shi da gajerun gabobi, sai ya yi amfani da wannan damar ya dauki hankalin mutane.

Za mu ci gaba da bibiyar duk wani takunsa don kawo wa masu karanta labarunmu sahihan bayanai da mu ka samo dangane da shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button