Labarai

Masu Adawa da komawar Wani Reshen CBN, Da FAAN, Zuwa Legas Kuskure ne – VP Shettima

Advertisment

Mataimakin Shugaban ƙasar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya soke masu adawa da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na mayar da wasu ma’aikatu da sassan babban bankin kasa (CBN) da hukumar kula da filayen jiragen sama na tarayyar Najeriya FAAN daga Abuja zuwa Legas, Yana mai cewa sun dauki matakin ne domin muradin al’ummar Najeriya gaba daya.

Masu Adawa da komawar Wani Reshen CBN, Da FAAN, Zuwa Legas Kuskure ne - VP Shettima
Masu Adawa da komawar Wani Reshen CBN, Da FAAN, Zuwa Legas Kuskure ne – VP Shettima

“Kwanan nan, Akwai masu adawa da matakin Gwamnatin tarayya kan shirin mayar da wasu ma’aikatu da sassan babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na Najeriya (FAAN) Daga Abuja zuwa Legas, ina so na tabbatar wa al’ummar jihar. Arewa cewa wannan mataki anyi shine domin maslahar ‘yan Nijeriya baki daya.

“Ajandar sabunta bege na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai yanke wata manufa ko shawarar da za ta zama na bangaranci ba, ko kuma za ta cutar da wani yanki na kasar nan, Don haka masu adawa da shirin mayar da wasu sassan ma’aikatun su daina, in ba haka ba suna aikata kuskure ne babba.” Inji VP Shettima

Advertisment
Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button