Malamai Sun Karyata Yiwuwar Dan Adam Ya Haifi Dabba A Zariya
A ranar litinin din wannan makon ne wata mata mai suna Murja ta shelantawa duniya cewa ta haifi wani dabba mai siffar Jaki a wata anguwa Tudun Wada karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.
Wannan lamarin ya ja hankalin mutane musamman a Arewacin Nijeriya saboda wannan lamari ne bako haihuwar dabba a zamantakewar Dan Adam kuma a al’adance.
Leadership hausa ta ruwaito Hakan ya sa manema labarai suka dukufa don jin ra’ayin masana akan lamarin.
Sheikh Aliyu Abdullahi Teleks babban malami ne kuma babban limami ne a masallacin Juma’a dake Tudun Jukun Zariya kuma shugaban majalisar malamai ta JBWIS jihar Kaduna a yayin da yakewa manema labarai jawabi akan lamarin haihuwar Dabba da malama Murja tayi a Tudun Wada Zariya.
“Gaskiya akwai shakku mai yawa a cikin wannan lamarin bisaga koyarwar addinin Islama domin wani jinsi baya haihuwar wani jinsi duk da cewa akwai masuyin sihiri amma koda hakan bai zama wannan lamarin ya zama gaskiya ba”.
Don hakan ne Shehin malamin ya ja hankalin jama’a akan irin wannan sihirin kuma ya bayar da misali da wani mutum da yace zai fitar da wani maciji a wata Daga da ake yawan hadari a zariya daga karshe lamarin ya tabbata ba kaskiya bane illla surkulle don haka yace, wannanma nan gaba jama’a zasu gane gaskiyar lamarin tunda ance ba haihuwar da tayiba Lamar yadda ake haihuwar da ta al’aura wannan mai bayar da maganin shafa cikin tayi kawai sai ga Dabba a matsayin shine abin dake cikin don haka ne malamin yayi kira da a guji yin imani abubuwan daka iya zama shirka.
Haka zalika mane ma labarai sun nemijin ta bakin likitocin kimiyar Dan Adan na asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello Zariya wato ( ABUTH)
Dakta Hasan Abubakar shine shugaban likitoci reshen asibitin Tudun Wada Zariya (medical Canter) dake karkashin asibitin koyarwa na jami’ar ta Ahmadu Bello Zariya.
Shima cewa yayi ” maganar Bil Adams ya haifi wani jinsi da ba Mutumba a ilmin zamani (Boko) hakan ya saba wa hankali amma akan sami mutum ya haifi mutum babu kafa ko wani sashi na jiki.
Don haka maganar cewa wata ta haifi Akuya ko Jaki a gaskiya wannan lamari akwai ayar tambaya akan lamarin.
Dakta Hasan Abubakar ya bayar da musali da cewa wata rana wani mutum mai dauke da ciwon kaba ya sanar damu cewa cutar (kabar) na damunsa amma wani ya bashi magani ya shafa a wajan (kabar) sai kadangare ya fito da nufin an jire masa (kabar) kuma hakan ba gaskiya bane illa sihiri da wasu sukeyi wajan bayar da maganin gargajiya.
Karshe likitan ya sanya ayar tambaya akan ahaihuwar wani dabba da malama Murja tayi.
Shima shahararen malaminnan mai suna (Malam Baiwa daga Allah) Wanda ke aiki da rundunar Yansan ta kasa a jihar Kaduna shima cewa yayi ” Gaskiya wannan bai zama abin mamaki ba domin Allah na iya yin komi don haka babu abin da yafi karfin Allah”
Shahararren malamin yayi suna wajan bayar da magani ga masu larurar ciwon Aljanu a kasa bani daya.
Tuni ya kara da cewa shi kanshi ya bayar da magani ga mai fama da kwatankwacin irin haka kuma aka sami waraka don haka babu abin da yafi karfin Allah.
Shiko dakta Ubale mai maciji Samaru masani kan al’amuran gargajiya a kasa baki daya cewa yayi .
” Tabbas Aljani kan shiga cikin jikin Bil Adama har ya haddasa masa ciwo mai tsanani don haka samun mutum ya haifi dabba ba abin mamaki bane don haka haihuwar da malam Murja tayi shi bai bani wani mamaki ba amma da ayi kokarin kaucewa shirks da surkullen wasu mutane da sukeso suyi kudi kota wani hali.
Ya zuwa hada wannan rahoto mutanene suke dandazo zuwa gidansu malama Murja don ganewa idansu abin mamaki.
Amma bincike ya nuna cewa shi Dabbar da Murja tace ta haifa ba haihuwarsa tayiba kamar yadda ake haihuwar kowa ta ( Farji) amma Murja ta tabbatar da cewa mai bayar da maganin shafata tayi akwai sai ga Dabban fado.
Haka zalika malama murja ta baiyana cewa takanje asibitin Dakta ( ) don yin awon ciki amma ba a ganin komi illa ruwa tsundum amma yau gashi Allah ya huna mata ikonsa taga abin dake cikinta.
Bicike ya tabbatar da cewa kashi 40 cikin 100 na kawo shakku akan lamarin bisa yadda lamarin ya zama abin almara.