Nasiru El-Rufai Yayi barazanar ficewa daga Apc idan Buhari ya bai gaggauta janye kalamansa ba
A yanzu nan muke samun wani labari wanda shafin Daily News Hausa sunka ruwaito a shafinsu na facebook inda suke cewa El-rufai yayi ikirarin ficewa daga jam’iyar matukar buhari bai gaggauta janye kalamansa ba.
“Za mu fice daga jam’iyyar APC matukar Buhari bai gaggauta janye kalaman sa na nuna goyon bayan bangaren Gwamna Mai Mala Buni kan shugabancin jam’iyyar APC
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa baza su taba yarda da matakin da Buhari yake shirin dauka na dawo da Mai Buni kan kujerar shugabancin jam’iyyar APC ba.
El-Rufa’i ya ce lallai doli ne Gwamna Mai Mala Buni ya sauka daga wannan matsayi tare da barma Gwamnan Neja Sani Bello.
Gwamnan ya yi barazanar barin jam’iyyar matukar akace za a ci gaba da yin wannan rashin adalci.”



