Hedikwatar ma’aikatar kuɗi ta Najeriya ta kama da wuta a Abuja


Babu tabbaci kan ko me ya jawo gobarar sai dai tuni ma’aikatan kashe gobara suka isa wurin.
Jaridar bbchausa a ruwaito mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato Abraham Paul inda ya ce ma’aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar.
A wani saƙo da ma’aikatar kuɗi da kasafi ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce gobarar ba ta yi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda ta ce wasu batira ne da aka keɓe suka kama da wuta a wani zaure da ke ƙasa a cikin hedikwatar ma’aikatar.
NewsFlash: The Federal Ministry of Finance HQ is not on fire as reported on social media. Rather, there was an incident on the corridor in the basement involving an isolated battery Pack (photo inset). It was quickly put out by the security personnel on duty. #FinMinNigeria pic.twitter.com/aNDzwF7kOc
— Ministry of Finance, Budget and National Planning (@FinMinNigeria) February 23, 2022
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



