Labarai

Dr Omar Atiq: Musulmi na farko da zai fara rike mukamin shugaban Kwalejin Likitoci ta kasar Amurka

Dr Omar Atiq: Musulmi na farko da zai fara rike mukamin shugaban Kwalejin Likitoci ta kasar Amurka
Dr Omar Atiq shine dan kasar Pakistan na farko da za a bawa mukamin shugaban kwalejin likitoci ta kasar Amurka (ACP), kuma zai zama likita na biyu wanda ba dan kasar ba da zai rike wannan mukami. Za a gabatar da wannan zabe, duk da cewa bashi da abokin hamayya a watan Janairun shekarar 2022.
Ganin irin sunan da kwalejin ke da shi a fadin kasar Amurka dama duniya baki daya, mambobin kasashe sama da 145 na duniya, za su sanya wannan abu cikin kundin tarihin kasar Pakistan.
Kimanin mutane 154,000, duka wadanda suka yi karatu a fannin lafiya, da kuma kwararrun likitoci da suka yi rijista a kwalejin.
Jaridar Labaranhausa ta kara da cewa Dr Omar Atiq, wanda yake farfesa ne a fannin likitanci da ilimin otolaryngology, an bashi mukamin shugaban ‘yan kwamitin gwamnonin kwalejin a shekarar 2019. Yana daya daga cikin ‘yan wannan kungiyar tun a shekarar 1993.
Ya yi karatu a kwalejin likitoci ta Khyber, da kuma jami’ar Peshawar dake kasar Pakistan, inda a nan ne ya samu kwalin digirin shi.
Dr Atiq wanda ke zaune a Arkansas, an bashi lambar yabo a duniya wajen ayyukan jin kai da yake yi, ya biyawa kimanin mutane 200 bashin da ake binsu a asibiti na $650,000, kimanin Naira miliyan 267, a watan Disambar shekarar 2019.

Bayan yayi aiki da kamfanin dake karbar basuka, ya gano cewa akwai mutane da dama da suke fama da matsalar rashin kudi da za su dauki nauyin rayuwar su, musamman ma yanzu da annobar coronavirus ta addabi duniya.
Ya tura wa marasa lafiya wannan labari mai dadi a lokacin Kirsimati, inda ya dinga aika musu kati, dauke da sakon cewa ya biya duka basukan da ake bin su.
A jikin katin Dr Atiq ya rubuta cewa cibiyar ciwon daji ta birnin Arkansas ta gano cewa mutane da dama basa iya daukar nauyin rayuwar su saboda haka da yawa daga cikin marasa lafiyan an biya musu bashin da ake bin su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA