Labarai
YANZU-YANZU: Majalisar Zamfara ta tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi
Advertisment
A zaman majalisar na yau Laraba, ƴan majalisa 20 cikin 21 ne su ka zaɓi a tsige Mataimakin Gwamnan bayan da a ka miƙa ƙudurin cire shi ɗin.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Talata ne dai kwamitin bincike da a ka kafa domin tuhumar Mahdi ɗin ya zauna jiya, amma kuma Mataimakin Gwamnan bai halarci zaman ba.
Sai dai kuma bayan da kwamitin ya miƙa rahoton da gaban majalisar a yau, sai mambobin su ka zaɓi su tsige Mataimakin Gwamnan.
Ƙarin bayani na nan tafe…
Ashe naziru sarkin waka wajen babansa yakoyo kalar rawanin dayakeyi kalli yadda mahaifinsa yayi SHIGAR alfarma
https://youtu.be/p_CAFWt8p14