Labarai

Yadda wata mata ta gane cewa mijinta mace ne bayan watanni 10 da auren su

Wata mata ta gano cewa mijinta da su ka kwashe watanni 10 da aure mace ne, duk da sun kudanci juna ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kamar yadda Daily Mail ta bayyana. LH na ruwaito

Matar wacce ‘yar kasar Indonesia mai suna NA, mai shekaru 22 ta maka mijinta a kotu wanda likitan kwakwalwa ne bayan ya kammala karatu a New York.

Ma’auratan sun fara haduwa ne a yanar gizo, inda mijin sunansa Ahmaf Arrafif a garin Jambi.

Bayan fara soyayyar a yanar gizo sai su ka hadu a fili inda Ahnaf ya kai wa NA ziyara ya kwashe mako daya tare da duba iyayenta marasa lafiya.

Bayan mako daya da haduwa, iyayen NA sun sanya musu albarka inda su ka amince da batun auren, Tribune News ta ruwaito.

Bayan watanni hudu da aurensu, ‘yan uwan NA sun fara zargin mijin nata.

Ahnaf bai taba gabatar mata da iyayensa ba kuma sun ci gaba da shirye-shiryen auren yayin da ya sanar da ita shi cikakken likita ne.

Mahaifiyar NA ta yi mamakin yadda Ahnaf bai taba cire sutturarsa ba kuma ba ya wanka a idan da mutane a gidan.

Bayan matar ta fuskancesa sai ya bayyana mata cewa yana da kuraje a kirjinsa ne kuma wata matsala ce a jikinsa.

Daga bisani, mahaifiyarta ta bukaci ya tube sutturarsa gaban kowa don ya tabbatar musu da cewa shi namiji ne.

Daga nan ne Ahnaf ya bayyana cewa shi mace ne, sunansa Erayani kuma ya yi karya ne akan komai har da aikinsa.

NA ta sanar da kotun yankin Jambi cewa bata taba zargin mace ne mijin da ta aura ba har sai da mahaifiyarta ta fara zarginsa.

A cewarta, sun dade su na kusantar juna kuma a tsawon lokacin hannunsa yake mata amfani da shi.

Yanzu haka Erayani tana kotu akan karyar da ta yi akan cewa ita likita ne kuma namiji ce ita.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button