[Bidiyo] Bidiyon da Hukumar NDLEA ta saki game da batun DCP Abba Kyari.
Bbchausa ta ruwaitoWata sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce bincikensu ya nuna cewa Abba Kyari na cikin wata ƙungiya da ke safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya.
Ta ƙara da cewa jami’an NDLEA sun gayyaci ɗan sandan don ya amsa tambayoyi game da zarge-zarge amma ya ƙi zuwa, “abin da ya sa muka yi wannan taron manema labaran kenan”.
“Ƙin amsa kiran hukumarmu da ya yi da ƙin ba mu hadin kai wajen bincike shi ne dalilin da ya sa muka yi taron manema labaran nan a yau.”
Idan ba a manta ba, a watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.
NDLEA ta kamen da aka yi da yawan mutanen da aka tsare a cikin wata 12 da suka gabata alama ce da ke nuna cewa a baya an raina girman matsalar tu’ammali da miyagun ƙwayoyi da ƙasar ke ciki, kafin Shugaba Buhari ya ƙarfafa hukumar NDLEA.
Amma ta ce a cikin wata 12 mafi yawan ƴan Najeriya sun yarda cewa ƙasar na cikin wata masifa ta tu’ammali da miyagun ƙwayoyi kuma suna yaba wa ayyukan NDLEA don daƙile hakan.
Sanarwar ta ce sai dai abin takaicin shi ne yadda wasu jami’an tsaron da ya kamata su haɗa hannu da NDLEA wajen daƙile wannan annoba su ne a gaba-gaba wajen karya dokar, ta wajen haɗa kai da su ana safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
Bayanan sirrin da muka samu sun sa hukumarmu ta yarda ɗari bisa ɗari cewa DCP Kyari ɗaya ne daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Brazil da Ethiopia da Nigeria, kuma yana buƙatar amsa tambayoyin da suka bijiro a kan wani batun safarar ƙwayoyi da yake jagoranta.
Ga bidiyon nan kasa.