Buhari Ya Zo Na 16 A Jerin Musulmi 500 Masu Daraja A Duniya
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na cikin jerin musulmi masu karfin fada aji a duniya, kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a Jordan ta bayyana.
Duk shekara cibiyar na wallafa sunayen musulmi 500 masu karfin fada aji a duniya.
Kuma a bincken da ta wallafa karo na 12 cibiyar ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne na 16 a jerin musulmi masu ƙarfin fada a ji a a duniya.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne musulmi mafi ƙarfin faɗa a aji a duniya. Sarki Salman na Saudiyya ne na biyu a duniya.
Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei ne na uku a jerin musulmi masu karfin fada a ji a duniya.
Cibiyar ta ce yawan musulmi a duniya an kiyasta cewa ya kai biliyan 1.9, kashi 26 na yawan al’ummar duniya.
Babban Shehin Malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ibrahim Saleh shi ne na 48 a duniya.
Sauran ƴan Najeriya da ke cikin jerin musulmi masu karfin fada a ji a duniya sun hada da Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.
Akwai kuma Shehin malamin Tijjaniya Sheikh Dahiru Bauchi da jagoran ƙungiyar Shi’a ta IMN Malam Ibrahim Zakzaky da kuma attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote.
Sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya sun hada da ƴan kwallon kafa inda cibiyar ta bayyana ɗan ƙwallon Masar Mohamed Salah a matsayin na 42.
Sauran ƴan ƙwallon da ke cikin jerin sunayen sun haɗa da Sadio Mane da Paul Pogba da Zinedine Zidane.
Cibiyar ta ce zaɓen mutanen ba ya nufin nuna goyon baya ga aƙidunsu ko amincewa da ra’ayinsu, illa auna girman karfin faɗa aji da suke da shi.
Sources:labaranduniya