Acire son rai A Karbi Gaskiya – Audu Bulama Bukarti zuwa ga ASUU
Mai sharhi akan yanayin tsaron nijeriya audu bulama bukarti ya kawo takaitaccen labarin samu kungiyar jami’oin nijeriya yayi bayyanin tiryan tiryan kan yadda asuu da gwamnati ke yawo da hankalin daliban tafiya akan yaji aikin inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda yake cewa.
“A CIRE SONRAI – A KARBI GASKIYA
Daga 1999 zuwa yau, ASUU ta yi yajin aiki sau 16 na jimillar tsawon watanni 51. A kowanne shekaru biyar, ASUU tana yajin kimanin shekara daya. Kenan a kowanne shekara biyar lakcara yana kar6ar albashin shekara daya ba tare da yayi aiki ba. Sannan kusan duk wanda ya gama jami’ar gwamnati a Najeriya, to yayi asarar kusan shekara guda saboda yajin aiki. ‘Yan siyasarmu ba su damu ba saboda basa tausayinmu. Su kuma ‘yan ASUU sun gaza fito da hanyar za ta 6ulle, kuma ba za ta cutar da dalibai ba.
Yanzu idan aka gama wata dayan nan, ASUU za su shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani. Su kuma ‘yan siyasa suna can suna harkokin siyasar 2023. Fisabillah, ta yaya mai tunani zai goyi bayan wannan? Ta yaya wannan zai zama aiki da hankali? Yanzu Buhari zai gagara barci saboda ana yajin aiki? Banda ministocin ilimi da dama wadanda ‘yan’yan ASUU ne, hatta shugabanni kasa biyu tsoffi ‘yan ‘yan ASUU sun gaza magance matsalar nan.
Amma abin mamaki, sai ka ga wadanda da kamar za su mutu don haushi idan aka yi yajin aiki, yanzu suna goyon bayan yajin aiki saboda jifa ya wuce kansu. Lokacin da ina dalibi ban goyi bayan yajin aiki ba. Lokacin da na koyar ban goyin bayan yajin aiki ba. Kuma yanzu ma bana goyon ba. Kuma wallahi da ASUU za ta bawa kowa za6i, malamai da dama za su je su koyar da dalibansu. Dalili kuwa shine: wannan salo bai magance matsalar ba kuma yana cutar da dalibai.
Mu cire sonrai da kiyayya ko soyayya, mu ji tsoron Allah, mu duba gaskiya. Daga kin gaskiya, sai bazama cikin daji. Ita kuma gaskiyan nan bata buqatar ado.”
Allah yasaka da alkhairi, bukarti Ni dalibi ne daga jahar Ahmadu Bello University zaria, nidan jahar Yobe ne kuma ɗan cikin garin gashua ina 400 level yanxu haka, duk mate namu sun gama dukda kasancewar munsha famar Strike tare amma su anyi musu rushing, mu Kuma yanxu nema muka sami shiga matakin qarshe muna murna amma qarshe Ga Asuu tashiga Strike.
Very sad.
Gaskiya yakamata gwabnati taduba bukatun ASUU don babu son rai a ciki.
Splendid good advice
Lalle munsan yajin aiki yana cutar da dalibai domin kuwa a karshe gomnati zata biya malamai kaga kenan dalibai sune da asara. To amma in ambita barawo….! Dominsuma malaman a dole suke tafiya yajin aiki. Ina mafita wacce hanya yakamata abi wacce bazata cutar dalibaiba?
Gaskiyane nima dalibin A.B.U Zaria daga jahar katsina kankara local govt to amma yakamata idan anbigi jaki abigi tirke lectures din nan susuke basu award yau gashi sune abun wulakantawa to allah yafiddamu.