Labarai

’Yan Bindiga Sun Auri Mata 13 Cikin Daliban FGC Yauri Da Suka Sace

’Yan Bindiga Sun Auri Mata 13 Cikin Daliban FGC Yauri Da Suka SaceKimanin wata takwas da sace dalibai ’yan mata daga makarantar sakandiren FGC Birnin Yawuri a Jihar Kebbi, har yanzu akwai sama da 10 a hannun ’yan bindigar da suka sace su.
Aminiya ta ruwaito cewa Hakan na faruwa ne duk da makuden kudaden fansarsu da aka biya da kuma yarjejeniyar musayar fursunonin da aka yi a lokuta daban-daban da masu garkuwar da su.
Sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar wa Aminiya cewa akwai akalla dalibai ’yan mata 13 da a yanzu haka ’yan bindigar suka aure su, wasu daga cikinsu ma har sun samu juna biyu.
A ranar 17 ga watan Yunin 2021 ne dai ’yan bindigar, wadanda yaran Dogo Gide ne, suka far wa makarantar sannan suka sace dalibai da dama da malamansu biyar.
Bayan Kashe Al’umma Da ‘Yan Bindiga Suka Yi A Yankin Shanga Dake Jihar Kebbi, Sun Sake Dawo Sun Bankawa Wani Kauye Wuta (bidiyo da hotuna)
Acire son rai A Karbi Gaskiya – Audu Bulama Bukarti zuwa ga ASUU
Aminiya ta kuma gano cewa tsakanin 11 zuwa 14 daga cikin daliban har yanzu suna hannun Dogo Giden, kuma namiji daya ne kawai a cikinsu.
Kimanin makarantu 10 ne ’yan bindiga suka kai wa hari a shekarar 2021 a jihohin Zamfara da Kaduna da Neja da kuma Kebbi.
Hare-haren tare da satar daliban sun biyo bayan wanda wani kasurgumin dan bindiga mai suna Auwal Daudawa ya fara jagoranta a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina a watan Disambar 2020, inda suka sace dalibai sama da 200.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button