Labarai

Ganduje ya yi amai ya lashe kan maganar “aika-aika”, inda ya ce ‘Ni da Kwankwaso ne mu ka gyara Kano’

Ganduje ya yi amai ya lashe kan maganar "aika-aika", inda ya ce 'Ni da Kwankwaso ne mu ka gyara Kano'
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa abokin burmin sa a siyasa, Sanata Ibrahim Shekarau gugar zana, inda ya ce shi (Ganduje) Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne su ka kawo ci gaban da a ke gani a Kano tun da ga 1999.
A tuna cewa bayan da rikici ya ɓarke tsakanin Ganduje da Kwankwaso, an jiyo gwamnan ya na cewa tsohon mai gidan nasa a siyasa ya yi “aika-aika”.
Daily Nigerian sun ruwaito cewa Kwatsam yau kuma, sai a ka ji gwamna Ganduje ya na yabawa Kwankwaso, in da ya ce tun daga 1999 zuwa yau, duk kun shaida cewa an yi wa Jihar Kano gyara fuska.
Da ya ke jawabi a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar a gidan gwamnati a yau Lahadi, Ganduje ya ƙi baiyana Shekarau a gwamnonin da su ka ciyar da Kano gaba, amma kuma sai ya ambaci Kwankwaso a cikin gwamnonin da su ka ciyar da Kano gaba.
“Wani Bafulatani da ya shafe sama da shekara 15 baya Kano, da ya dawo Kano ya ga canji a jihar, sai ya rude ya ce ko Kano ce da ya sani.
“Wasu jama’a a kusa da shi suka amsa masa da cewa a’a wannan sabuwar Kano ce, sai ya tambaye su wane ne ya canza fuskar Kano? Sai jama’a suka amsa masa cewa Kwankwaso da Ganduje ne su ka gina sabuwar Kano,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa nasarar kotun ɗaukaka ƙarar da ɓangaren sa ya samu ba zai sanya su saki jiki su ƙi ƙarfafa APC a jihar ba, inda ya ce za a samar da sabbin tsaruka domin ƙara wa jam’iyar ƙarfi a kakar zaɓe mai zuwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button