Labarai

Wata mata a Najeriya ta gina wa mijinta Masallaci sadaqatul jariya (bidiyo)

Wata mata ‘yar Najeriya ta gina wa mijinta, Farfesa Gidado Tahir masallaci a Yola jihar Adamawa.

Wata ‘yar uwa, Zahra Danejo, ta bayyana hakan ta hanyar X a ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta.

Yar uwata  ta gina wannan masallaci a Yola a matsayin Sadaqatul Jariya domin girmama mijinta, kawuna, Farfesa Gidado Tahir. Idan wannan ba soyayya ta gaskiya bace to bansan menene ba. Allah ya albarkacina… Allah ya jikansa da Jannah Amin”

Wata mata a Najeriya ta gina wa mijinta Masallaci sadaqatul jariya
Farfesa Tahir Gidado

Late farfesa Tahir, babban sakatariyar zartaswar UBEC, ya rasu a shekarar 2022.

Ga bidiyon masallacin nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button