Labarai

Aure arha gare shi, sai dai idan dan karya ne kai: Hotunan auren matashin da ya kashe N20,500

Aure arha gare shi, sai dai idan dan karya ne kai: Hotunan auren matashin da ya kashe N20,500
Wani dan Najeriya mai suna Ani Nnamdi Chris, ya angwance da matar sa yayin da suka yi kwarya-kwaryan taro wanda suka gabatar a sirran ce, legit.ng ta ruwaito.
Yayin wallafa hotunan shagalin da ya guduna a 4 ga watan Fabrairu, Chris ya ce, gaba daya abinda ya kashe na bikin N20,500 ne.
Mutumin cikin alfahari ya kara da bayyana yadda ya tarbi mutane 10 kacal wadanda suka hada da shi da matar tasa, inda ya ce aure bashi da tsada ya danganta da karfin ka
.

Wani sabon ango dan Najeriya mai suna Ani Nnamdi Chris ya ba wa duniya mamakin yadda ya angwance da masoyiyar sa, inda suka gabatar da wani dan kwarya-kwaryar taron sirri.
Chris ya wallafa hotunan dan karamin shagalin bikin, wanda ya gabata a 4 ga watan Fabrairu a shafin sa na Twitter, inda ya bayyana gaba daya abinda ya kashe a N20,500 inda yace ya biya N15,500 a matsayin kudin rijista a kutu, inda ya bada N5,000 ga mai rigistar ya sha ruwa.Aure arha gare shi, sai dai idan dan karya ne kai: Hotunan auren matashin da ya kashe N20,500 Aure arha gare shi, sai dai idan dan karya ne kai: Hotunan auren matashin da ya kashe N20,500
A cewar Chris aure babu tsada, dan kwarya-kwaryar taron ya biyo bayan daurin auren a kotu ne, inda ya kunshi mutane 10 kacal duk da shi da matarsa.
Ga tsokacin jama’a a karkashin wallafar tasa;

@Sammygyang ya ce: ” Kana da dabara. Ina taya ka murna! Kayi wa auren ka tanadi ba biki ba. Mutane da yawa suna almubazzaranci a bukukuwan su suke yi duk don su birge tarin mutanen da basa kaunar su. Amma idan auren ya lalace, kashi 80 cikin 100 na mutanen sune zasu fara gulmarsu a shagon aski da gidajen giya.”

@emelda_ ani ya rubuta: “Kawu na Nnamdi, kamar yadda naji dadin abinda kayi, baka bada cikakken labarin ba. Kada kasa wadan nan kananan yaran su yi tunanin dubu 30 zata ishe su aure. ” Yanzu, baka bamu labarin yadda shagalin bikin al’adan ya kaya ba. Ina da tabbacin ka biya sadakin ta.”

@ejyvik yace: ” Ina jan kunnen aboki na da matar sa da suka sa ni na biya dubu 160 na ankon da ban sa ba, idan suka yi kuskuren nuna sun gaji da auren, su fara tunanin biya na kudi na har da riba, Ubangiji ya albarkaci gidan auren ku.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button