Duniya Ina zaki Damu ! An Sake Ceto Ran Mutumin Da Anka Daure Shekara 30 A kano
Yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ceto wani mutum mai shekaru 55 da ‘yan uwansa suka ɗaure na tsawon shekaru 30 sakamakon yana da taɓin hankali.
Wani ɗan kare haƙƙin bil adama Sani Shuaibu ya shaida wa BBC cewa mutumin ya shafe shekaru yana cikin wahala, inda aka ɗaure shi jikin wani ƙaton ƙarfe a cikin wani ɗaki da bai da ƙofa ko kuma taga.
Hakan ya sa ya faɗa wa ‘yan sanda halin da mutumin yake ciki bayan ya samu labari kan mutumin, kuma suka ceto shi tare da ‘yan sanda a garin Rogo da ke Kano.
“Mutumin yana da taɓin hankali kuma ya fara faɗa, a maimakon a nemo masa magani tun a 1990, sai mahaifinsa ya yanke shawarar ɗaure shi,” in ji Shu’aibu.
Bayan mahaifin mutumin ya rasu a shekarun baya, sai ‘yan uwansa suka ci gaba da kulle mutumin, amma a halin yanzu, an sake shi. Wasu daga cikin makwaftansa da suka san halin da yake ciki sun taimaka wurin ceton, in ji shi.
Mutumin mai shekaru 55 a halin yanzu yana babban asibitin garin Rogo inda a nan ne yake karɓar magani, inda kuma tuni aka tafi da ‘yan uwansa wurin ‘yan sanda.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin kuma ya ce ana gudanar da bincike.
Wannan ne aikin ceto na uku cikin ƙasa da makonni biyu da aka yi na mutane masu buƙata ta musamman da ‘yan uwansu suka yi musu ɗaurin talala.