Aisha Aliyu Tsamiya Ta fitar da sanarwa akan Aurenta
BAYA ta haihu. Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ba a gobe Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 ba ne za a ɗaura mata aure kamar yadda aka yaɗa a soshiyal midiya.
Fim magazine ne ta ruwaito wannan labari Wannan sabuwar sanarwar ta biyo bayan yaɗa wani katin gayyatar aure ne wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ana cewa na auren jarumar ne.
A katin, an nuna cewa fitacciyar jarumar za ta yi aure a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022.
A katin, wanda mujallar Fim ta gani, an bayyana sunan sahibin nata, wato Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano.
Tun da labarin auren ya ɓulla a soshiyal midiya abokan sana’ar A’isha su ka shiga yi mata fatan alheri, inda kusan dukkan su sun ɗora hoton ta tare da katin auren.
To amma ɗazu ɗazun ban Aisha Tsamiya ta hau Instagram ta rubuta cewa, “Assalamu alaikum, jama’a barkan mu da warhaka. Na gode da addu’o’in ku da fatan alkhairi, na ji daɗi sosai, amma aure na ba 25th ga wannan watan ba ne, sai next month in-sha Allah……Na gode Allah ya saka da alkhairi.”
Wannan sanarwar, wadda Tsamiya ta yi a shafin ta na Instagram mai mabiya sama da miliyan ɗaya, ya ba mutane da dama mamaki.
A’isha Tsamiya dai ta na ɗaya daga cikin jaruman Kannywood da wasu ke ganin kamar sun ƙi aure ne.
Wasu kuma su na yi mata kallon mayaudariya, don su na cewa akwai lokacin da ta yaudari darakta Mu’azzam Idi Yari da kuma jarumi kuma mai bada kayan sawa (costumier) Sadiqu Atis.
Haka kuma a ‘yan shekarun baya har an gama maganar auren ta da wani attajiri da ke Jihar Kebbi, wanda aka sa bayan ta dawo daga aikin Hajji za a yi bikin, ta na dawowa sai kuma labari ya canza, aka fasa auren. Wasu na cewa ita ce ta ce ta fasa auren, yayin da wasu su ka riƙa cewa shi ne ya fasa saboda wasu dalilai.
Kafin wannan lokaci, an ɗauki tsawon lokaci ba a jin ɗuriyar jarumar a Kannywood, musamman a yanzu da masana’antar ta koma cin kasuwa a YouTube.
Allah sa hakane yafi alheri saura gabon da sadau allah kawo naku in kuna bukata
Inna miki fatan Alheri amma ki dauki darasi ga yaruwar Hajiya Safiya Musa Wanda tana chikin yin film tayi aure kuma ya hakura da rayunwan. Don Allah Inna miki fatan Alheri da zaman lafiya.
Allah yasa ayi a sa,a aishatu tsamiya, sauran yan uwanki da basuyiba Allah kawo musu nasu kusa suma
Inayiwa kowa fatan alkhairi
Allah yasa ayi ,sa,a yakuma baku zaman lafiya my best female kanywood actres