Kannywood

Datti Assalafiy yayiwa Rarara wakin babban bargo akan maganganun sa

Advertisment

Shahararren marubucin nan kuma masoyin Buhari Datti Assalafiy yayi martani mai zafi biyo bayan kallon hirar mawaki dauda kahutu rarara inda yake cewa.

Bidiyo da aka nuna Rarara a gaban ‘yan jarida yana zagin Shugaba Buhari cewa shine ya kashe kasa gaskiya ne bidiyon

Lallai ko a mafarki banyi zaton Rarara zai juya wa Shugaba Buhari baya ba, domin duk abinda Rarara ya samu na arziki sanadin Buhari ne, amma da yake butulu ne yau Buhari yake zagi

Dama haka dabi’ar mawaka, maroka da karuwai suke, suna bin wanda suke tunanin zasu tatsi kudi daga gareshi ne

To amma ni kaf a cikin maganganun Rarara babu wanda ya bata min rai kamar cewa da yayi wai Wallahi wata ukun Bola Tinubu yafi shekara 8 din Buhari

Datti Assalafiy yayiwa Rarara wakin babban bargo akan maganganun sa
Datti Assalafiy yayiwa Rarara wakin babban bargo akan maganganun sa

Rarara nace a gidan Babarka kenan?
Shin Rarara kana da imani da cikakken hankali kuwa?

Ka dubi halin bala’in yunya da talauci da aka jefa talakawan Arewa sakamakon janye tallafin man fetur da Tinubu yayi amma a haka kake cewa wai wata uku yafi shekaru 8 din Gwamnatin Buhari

Wallahi na dena ganin laifin ‘yan Kwankwasiyya da suke caccakar Rarara, tabbas sun yi daidai, kuma da ina yin ashar tabbas Wallahi da sai na dura wa Rarara buhun ashar yau din nan ko zan ji sanyi a raina, mugu kawai marar imani da tausayi

Babu abinda zamu ce tsakanin mu da wanda yake cewa wata ukun Tinubu yafi Shekara 8 din Buhari sai Allah Ya isa

Ina Ministocin Buhari wadanda suka yi ta janyo Rarara cikin ofis dinsu suna bashi kwangiloli Kukayi watsi da masayoyan Buhari na gaskiya? to yau ga sakamakon nan

Rarara lokacinka ne, amma kana da iyaka watan watarana, sai dai zai yi wahala kayi kyakkyawan karshe da wannan halin naka

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button