Kannywood

Falalu dorayi yayiwa shugabanni Wankin babban bargo

Advertisment

Babban mai bada umurni da shirya fina finai a masana’antar kannywood falalu dorayi inda yayi rubuci mai ban takaici da alhini akan yan uwanmu yan arewa da akeyiwa kisan gila wanda ya nuna gazawar shugabanni inda yayi jawabi kamar haka.

Gazawar SHUGABANNI.
kullum kara bayyana take a tsakanin zababbu da wadanda aka nada don rike wasu madafai.

Abin takaici ne abin Allah wadarai,
-Kuna zaune a gida a shigo a kashe ku, a farma iyalanku mata.
-Kuna kan hanya a tare a debe ku a kashe na kashewa.
-Ku bar gari domin gudun tsira a tare ku a KONE KU.
-Kuyi noma domin samun abinci, a kone gonar da amfanin cikinta. Ko kuma kai da gonarka sai DAN TA’ADDA Ya saka muku haraji sannan ku noma ko girbe abin da kuka Namiji.

Shugabannin Yanzu muddi datti bai hau kan rigar su ba, basa gane ana guguwa a garinsu.

Tsakanin KISAN RAI, FYADE, hana Kasuwancin, da KONE abinci a GONA, da kone MUTANE da RANSU duk babu wanda Gwamnatin JAHA da ta KASA da wakilansu ba su san yana faruwa ba.

Idan kanaso kaga karfin ikonsu to kaba kujerarsu ko ku kuma Jam’iyarsu.

Allah mun tuba, ka kawo mana agajin KA. Ya As-Samadu ka taimakemu wajan zaben nagari masu kishinmu a zabe mai zuwa. Amin.”

Yayi wannan rubutu ne akan kone motar yan asalin jahar Sakkwato da sunka fito karamar hukumar sabon birni wani kauye mai suna gidan bawa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button