Kannywood

Na Shiga fim domin nayi Fice duniya ta sanni – Jaruma Aisha Sani

Jaruma Kuma mawakiya a Masana’antar shirya fina-finai na Hausa Kannywwod Amina Sani, ta bayyana manufar da ta kawo ta cikin harkar fim, wanda ta ce neman suna domin ita ma Duniya ta san da zaman ta.

Amina Sani ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimokaradiyya, kamar yanda aka saba kawo muku tattaunawa da su masu wannan sana’a ta fim.
“Kamar yanda kowa ya ke da manufa ta shigar sa duk wani abu da ya ke so ya fara, to nima haka na zo da tawa manufar a wannan Masana’anta, don haka Ni dai na zo ne domin na samu daukaka na yi suna, kuma duniya ta sanni,” acewarta

Amina ta ce “Kowa ya na son ya daukaka duniya ta san shi don haka nima na fito domin na bayyana kaina a sanni Kuma na samu daukaka, don haka ne ma na shigo harkar fim, Kuma Alhamdulillahi a yanzu ina ganin nasara a Kan abun da na sa a gaba, domin a yanzu na fito a finafinai da dama, Kuma na fito a wakoki masu yawa, wanda wasu Ni na dauki nauyin shirya su, wasu Kuma aiki a ke ba Ni na ke yi”.

Dimokuradiyya: Amma ke manufar ki ta bambanta da sauran Jarumai da su ke cewa sun zo ne don su fadakar ta hanyar fim ya abun yake?

Sai ta ce” To ai ka San kowa da irin ta sa manufar, Ni Kuma tawa na ke fada maka, shi ya sa ma Ni ban boye maka ba, ko da kuwa ta bambanta da ta wasu Ni iya abun da ya ke zuciyata Kenan.

“Ko za ka yi fadakarwa sai ka samu daukaka ne mutane za su rinka sauraron ka don haka na ke so duniya ta sanni, Kuma ina fatan nan gaba kadan burina zai Kai ga cika, don haka ina fatan masoya na za su taya Ni da addu’a don na samu na cimma nasarar abun da na sa a gaba”.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button