Labarai

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta tabbatar da Ɗanzago a matsayin Shugaban APC a Kano, ta kuma umarci tsagin Ganduje da ya biya naira miliyan 1

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta tabbatar da Ɗanzago a matsayin Shugaban APC a Kano, ta kuma umarci tsagin Ganduje da ya biya naira miliyan 1Wata babbar kotu a Abuja ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu ta tabbatar da cewa ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau na jam’iyar APC ya yi sahihin zaɓe na shugabannin jam’iya a matakin karamar hukuma da mazaɓu a jihar.

A ranar 30 ga watan Nuwamba ne dai alƙalin ya amince da duk ƙorafe-ƙorafe da tsagin Shekarau ya yi ga kotun na cewa ɓangaren Ganduje bai yi zaben shugabannin jam’iya na mazaɓa ba.

Da ga bisani sai ɓangaren Ganduje ya garzaya kotu inda ya shigar da ƙara ya na neman kotun ta daka da sauraron ƙarar ya a kuma janye matakin da ta ɗauka a kan zaɓen shugabannin jam’iya na mazaɓa.

Da ya ke yanke hukunci a kan ƙarar ta ɓangaren Ganduje, Mai Shari’a ya kori ƙarar ta su ya kuma caje su Naira miliyan 1 sakamakon ƙara mara tushe da kuma bata lokacin ɗaya ɓangaren na su Shekarau.
Ƙarin bayani na nan tafe…
Daga : Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA