Bidiyo :Subhanilillahi ! An Kulle Matashi tsawon shekaru 15 A Kano ( A Yau anka samu wannan Rahoto)
Rahoto daga Rabiu biyora wannan bala’i da me yayi kama Malam , Allah ya sawake.
Yau lahadi hukumar yan sandan jihar Kano suka samu nasarar kubuto da matashin daga inda ake tsare dashi…
Da alama dai akwai bukatar a fara Operation Gida Gida a Kano…
Matashin dan shekara 31 dake zaune a unguwar Sheka Kano, mahaifinsa ya daureshi a gidansu har tsawon shekaru 15, duk da rahonni sun bayyana cewa Mahaddacin al’qur’ani ne, amma mahaifinsa ya daureshi akan wasu dalilan da shi kadai ya sani…
Matashin ya samu yanci ne bayan da hukumar yan sandan kano ta samu rahoto akan lamarin, inda SP Baballo Majia da DPO din Nassarawa suka jagoranci kubuto da matashin, inda yanzu haka yake asibitin Nassarawa domin kulawa da lafiyarsa….
Allah ya kyauta….
Ga bidiyon nan kasa.