Labarai

Matashin Da Tsinci Kudi Dala $50k Kimanin Naira Miliyan 25 Ya Mayarwa Mai kudi Abinsa

Matashin Da Tsinci Kudi Dala $50k Kimanin Naira Miliyan 25 Ya Mayarwa Mai Abu
Shahararren marubuci nan a kafar sada zumunta Datti Assalafy ya samu sauki inda yayi zazzabi mai zafi amma yanzu alhamdulillahi ya samu sauki a safiyar yau ya kawomuna wani labari mai dauke da darasi a cikinsa sosai kan wani matashi wanda ya nuna har gobe na kwarai basa karewa inda shi kuma ya sanya ya samu alkhairi sosai a cikin wannan abun da ya aikata kamar yadda zaku Datti Assalafy ya bayyana .
AKWAI DARASI ANAN
Daga Kasar Liberia Matashi Emmanuel Tuloe ya tsinci kudi dalar Amurka dubu hamsin ($50,000) kimanin Naira Miliyan 25 , bayan ya tsinci kudin sai bai rike ba, yabi diddigi ya mayar wa mai kudin abinsa
Labarin matashin ya yadu sosai a duk manyan kafofin watsa labarai na duniya ba iya Kasar Liberia ba, akwai masu son zuciya da suke ganin wai matashin yayi wauta da ya tsinci wadannan makudan kudade ya mayarMatashin Da Tsinci Kudi Dala $50k Kimanin Naira Miliyan 25 Ya Mayarwa Mai Abu
Shugaban Kasar Liberia George Weah ya sa an kira matashin domin ya jinjina masa, sannan ya bashi kyautar kudi dalar Amurka dubu goma ($10,000) kimanin Naira Miliyan 5
Shugaban Kasar Liberia bai barshi haka ba, ya bashi kyautar mashina guda 2, sannan ya dauki nauyin karatunsa har zuwa matakin digiri na biyu, kuma duk wata za’a bashi albashin dalar Amurka dari biyar ($500) kimanin Naira dubu dubu dari biyu da hamsinMatashin Da Tsinci Kudi Dala $50k Kimanin Naira Miliyan 25 Ya Mayarwa Mai Abu
Darasi, a rayuwa duk abinda ka sameshi ta hanyar haram inda zakayi hakuri kabi ta hanya mai kyau, ka nema ta hanya mai kyau, sai Allah Ya baka ta hanyar halal
Inda wannan matashin bai mayar da kudin ba, kudin ba zai taba masa albarka ba, zai kama hanyar shashanci ya fara hulda da karuwai, karuwa zata jashi su kashe kudin a hotel, tsanani shekara guda kudin ya kare, yanzu da yayi hakuri ya samu mafi alherin abinda ya tsinta ya mayarMatashin Da Tsinci Kudi Dala $50k Kimanin Naira Miliyan 25 Ya Mayarwa Mai Abu
Muna fatan Allah Ya bamu halal, Ya nesanta haram daga garemu”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button